32 Ga duk wanda ka iske gumaka a wurinsa, a kashe shi. Yanzu a nan gaban danginmu, ka nuna abin da nake da shi wanda yake naka, ka ɗauka.” Ashe, Yakubu bai sani Rahila ce ta sace su ba.
33 Laban ya shiga alfarwar Yakubu, da ta Lai'atu, da na kuyangin nan biyu, amma bai same su ba. Sai ya fita daga alfarwar Lai'atu, ya shiga ta Rahila.
34 Ashe, Rahila ta kwashe gumakan ta zuba su cikin sirdin raƙumi, ta zauna a kansu. Laban ya wawaka alfarwar duka, amma bai same su ba.
35 Sai ta ce wa mahaifinta, “Kada ubangijina ya yi fushi da ban iya tashi ba, don ina al'adar mata ne.” Ya kuwa bincike, amma bai sami gumakan ba.
36 Yakubu ya husata, ya yi wa Laban faɗa, ya ce wa Laban, “Wane laifi na yi, mene ne zunubina da ka tsananta bina?
37 Ko da yake ka wawaka dukan kayayyakina, me ka samu na gumakanka a ciki? A tabbatar a nan yau a gaban dangina da danginka, su yanke shari'a tsakanina da kai.
38 Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba.