10 ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu.
11 Ka cece ni ina roƙonka daga hannun ɗan'uwana, wato daga hannun Isuwa, gama ina jin tsoronsa, kada ya zo ya karkashe mu duka, 'ya'ya da iyaye.
12 Gama ka riga ka ce, ‘Zan yi maka alheri, in kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda ba su lasaftuwa saboda yawansu.’ ”
13 Ya yi zango a nan a wannan dare, ya kuwa bai wa ɗan'uwansa Isuwa kyauta daga cikin abin da yake da shi,
14 awakai metan da bunsurai ashirin, tumaki metan da raguna ashirin,
15 raƙuman tatsa talatin tare da 'yan taguwoyi, shanu arba'in da bijimai goma, jakai mata ashirin da jakai maza goma.
16 Waɗannan ya sa su a hannun barorinsa ƙungiya ƙungiya, ya ce wa barorinsa, “Ku yi gaba, ku ba da rata tsakanin ƙungiya da ƙungiya.”