22 A wannan dare kuwa ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da kuyanginsa biyu da 'ya'yansa goma sha ɗaya ya haye mashigin Jabbok.
23 Ya ɗauke su ya haye da su rafi, haka kuma ya yi da dukan abin da yake da shi.
24 Aka bar Yakubu shi kaɗai.Sai wani mutum ya kama shi da kokawa har wayewar gari.
25 Sa'ad da mutumin ya ga bai rinjayi Yakubu ba sai ya taɓa kwarin kwatangwalonsa, sai gaɓar kwatangwalon Yakubu ta gulle a lokacin da yake kokawa da shi.
26 Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.”Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
27 Sai ya ce masa, “Yaya sunanka?”Ya ce, “Yakubu.”
28 Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”