28 Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
29 Sa'an nan Yakubu ya tambaye shi, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.”Amma ya ce, “Don me kake tambayar sunana?” A nan mutumin ya sa masa albarka.
30 Saboda haka Yakubu ya sa wa wurin suna Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.”
31 Rana ta yi sama a sa'ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa.
32 Saboda haka, har wa yau, Isra'ilawa ba sā cin jijiyar kwatangwalo wadda take a kwarin kwatangwalo, domin an taɓi kwarin kwatangwalon Yakubu ta jijiyar kwatangwalo.