1 Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa'ad da kake guje wa ɗan'uwanka Isuwa.”
2 Sai Yakubu ya ce wa iyalin gidansa da dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku kawar da gumakan da suke wurinku, ku tsarkake kanku, ku sāke rigunanku,
3 sa'an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.”
4 Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.
5 Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin 'ya'yan Yakubu.
6 Sai Yakubu ya zo Luz, wato Betel, wadda take cikin Kan'ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi.
7 A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa'ad da yake guje wa ɗan'uwansa.