4 Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.
5 Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin 'ya'yan Yakubu.
6 Sai Yakubu ya zo Luz, wato Betel, wadda take cikin Kan'ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi.
7 A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa'ad da yake guje wa ɗan'uwansa.
8 Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut.
9 Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka.
10 Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra'ila.” Don haka aka kira sunansa Isra'ila.