22 Sai Ra'ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.
23 Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu.
24 Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.
25 Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu.
26 Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi.
27 Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa.
28 Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!”Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”