11 “Ya Ubangiji, wane ne kamarka a cikin alloli?Wa yake kamarka a cikin ɗaukaka da tsarki?Mai banrazana cikin mafifitan ayyuka, mai aikata mu'ujizai.
12 Ka miƙa dantsen damanka, ƙasa ta haɗiye su.
13 Da tabbatacciyar ƙaunarka, ka bi da jama'arka da ka fansa,Ka bi da su da ƙarfinka zuwa tsattsarkan mazauninka.
14 Al'ummai suka ji suka yi rawar jiki,Tsoro ya kama mazaunan Filistiya.
15 Sarakunan Edom suka tsorata,Shugabannin Mowab suna rawar jiki,Dukan mazaunan Kan'ana sun narke.
16 Tsoro da razana sun aukar musu,Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse,Har jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,I, jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,
17 Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka,Wurin, ya Ubangiji, da ka maishe shi tsattsarkan mazauninka,Tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, wanda ka kafa da ikonka.