13 Da tabbatacciyar ƙaunarka, ka bi da jama'arka da ka fansa,Ka bi da su da ƙarfinka zuwa tsattsarkan mazauninka.
14 Al'ummai suka ji suka yi rawar jiki,Tsoro ya kama mazaunan Filistiya.
15 Sarakunan Edom suka tsorata,Shugabannin Mowab suna rawar jiki,Dukan mazaunan Kan'ana sun narke.
16 Tsoro da razana sun aukar musu,Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse,Har jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,I, jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,
17 Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka,Wurin, ya Ubangiji, da ka maishe shi tsattsarkan mazauninka,Tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, wanda ka kafa da ikonka.
18 Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”
19 Gama sa'ad da dawakan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa suka shiga bahar, Ubangiji ya komar da ruwan bahar a bisansu, amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busassiyar ƙasa ta tsakiyar bahar.