4 Walƙiyarsa kamar hasken rana ce,Haske yana haskakawa daga gare shi,A nan ne ya lulluɓe ikonsa.
5 Annoba tana tafe a gabansa,Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.
6 Ya tsaya, ya auna duniya,Ya duba, sai ya girgiza al'umman duniya.Sa'an nan madawwaman duwatsu suka farfashe,Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya.Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.
7 Na ga alfarwan Kushan suna cikin azaba,Labulen ƙasar Madayana suna rawar jiki.
8 Ya Ubangiji, ka hasala da koguna ne?Ko kuwa ka yi fushi da koguna?Ko kuwa ka hasala da teku ne,Sa'ad da ka hau dawakanka, kana bisa karusarka ta nasara?
9 Ka ja bakanka,Ka rantsar da sandunan horo.Ka rarratsa duniya da koguna.
10 Duwatsu sun gan ka, sun ƙame,Ruwaye masu hauka suka gudu.Zurfi kuma ya ta da muryarsa,Raƙuman ruwansa sun tashi.