15 Ubangiji ya ce, “Wane iko ƙaunatacciyata take da shi cikin Haikalina, da ya ke ta aikata mugayen ayyuka? Ko alkawarai da naman hadayu za su iya kawar miki da ƙaddararki, har da za ki yi taƙama?
16 Dā na kira ki itacen zaitun mai duhuwa, kyakkyawa, mai kyawawan 'ya'ya, amma da ƙugin babbar iska za a cinna miki wuta, za ta kuwa cinye rassanki.”
17 Ubangiji Mai Runduna, wanda ya dasa ku, ya hurta masifar da za ta same ku saboda muguntar da mutanen Isra'ila da na Yahuza suka yi, suka tsokane ni in yi fushi saboda suna ƙona wa Ba'al turare.
18 Ubangiji ya sanasshe ni,Na kuwa sani,Sa'an nan ya nuna mini mugayenayyukansu.
19 Amma ina kama da lafiyayyen ɗanrago,Wanda aka ja zuwa mayanka,Ashe, ni suke ƙulla wa munafuncin!Ni kuwa ban sani ba, da suke cewa,“Bari mu lalatar da itacen duk da'ya'yansa.Bari mu datse shi daga ƙasar masurai,Har da ba za a ƙara tunawa dasunansa ba.”
20 Amma ya Ubangiji Mai Runduna,mai shari'ar adalci,Kakan gwada zuciya da tunani,Ka yarda mini in ga sakayyar da zaka yi mini a kansu,Gama a gare ka na danƙamaganata.
21 Saboda haka ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka, da suka ce, “Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji, in ba haka ba, da hannunmu za mu kashe ka.”