1 Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka.Duk da haka zan bayyana ƙarata agabanka,Me ya sa mugaye suke arziki cikinharkarsu?Me ya sa dukan maciya amana sukezaman lafiya,Suna kuwa ci gaba?
2 Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa,Suna girma, suna kuma ba da'ya'ya,Sunanka na a cikin bakinsu, ammakana nesa da zuciyarsu.
3 Amma kai, ya Ubangiji, kana sane dani, kana ganina,Kai kanka kake gwada tunanina.Ka jawo su kamar tumaki zuwamayanka,Ka ware su domin ranar yanka.
4 Sai yaushe ƙasar za ta dainamakoki,Ciyawar kowace saura kuma ta dainayin yaushi?Saboda muguntar mazaunan ƙasarne dabbobi da tsuntsaye sukaƙare,Domin mutanen suna cewa, “Ba zaiga ƙarshenmu ba.”
5 Ubangiji ya ce,“Idan kai da mutane kun yi tserenƙafa sun gajiyar da kai,Yaya za ka iya gāsa da dawakai?Idan ka fāɗi a lafiyayyiyar ƙasa,Ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?