6 Yaro da babba za su mutu a wannan ƙasa, ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi baƙin ciki dominsu ba. Ba kuwa wanda zai tsaga jikinsa ko ya aske kansa ƙwal dominsu.
7 Ba wanda zai ba mai makoki abinci don ya ta'azantar da shi saboda mamacin, ba kuma wanda zai ba shi abin sha don ya ta'azantar da shi saboda mahaifinsa ko mahaifiyarsa.
8 “Kada kuma ka shiga gidan da ake biki, ka zauna ka ci ka sha tare da su.
9 Gama ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan sa muryar murna, da ta farin ciki, da ta ango, da ta amarya, su ƙare a wurin nan a idonka da zamaninka.
10 “Sa'ad da ka faɗa wa mutanen nan wannan magana duka, za su kuwa ce maka, ‘Me ya sa Ubangiji ya hurta wannan babbar masifa a kanmu? Mene ne laifinmu? Wane irin zunubi muka yi wa Ubangiji Allahnmu?’
11 Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, ‘Domin kakanninku sun rabu da ni, sun bi gumaka, sun bauta musu, sun yi musu sujada. Sun rabu da ni, sun ƙi kiyaye dokokina.
12 Ku kuma kun yi laifi fiye da na kakanninku. Kowannenku kuwa ya bi tattauran mugun nufin zuciyarsa, yana ƙin kasa kunne gare ni.