7 Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’
8 “Sai ka faɗa wa wannan jama'a, ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, na sa tafarkin rai da na mutuwa a gabanku.
9 Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa.
10 Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.’ ”
11 “Sai ka faɗa wa gidan sarautar Yahuza cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji,
12 Ya gidan Dawuda, ni Ubangiji na ce,Ku aikata adalci kowace safiya.Ku ceci wanda aka yi masa ƙwacedaga hannun mai matsa masa,Don kada hasalata ta tashi kamarwuta,Ta yi ƙuna, har ba mai iya kasheta,Saboda mugayen ayyukanku.
13 Ga shi, ina gāba da ku, ya kumazaunan kwarin,Ya dutsen da yake a fili,’ in jiUbangiji.‘Ku da kuke cewa, wa zai iyagangarowa wurinku,Ko kuwa wa zai shiga wurinzamanku?