1 Haka Ubangiji ya faɗa, “Ka tafi ka gangara zuwa gidan Sarkin Yahuza, ka faɗi wannan magana a can,
2 ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya Sarkin Yahuza, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda kai da barorinka, da mutanenka waɗanda suke shiga ta ƙofofin nan.
3 Haka Ubangiji ya ce, ka yi gaskiya da adalci, ka ceci wanda ake masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka cuci baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, kada kuma ka zubar da jinin marasa laifi a wannan wuri.
4 Hakika idan ka kiyaye wannan magana, sa'an nan sarakunan da za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan gida da karusai da dawakai, su da barorinsu da jama'arsu.
5 Amma idan ba ka kula da waɗannan zantuttuka ba, na rantse da zatina,’ in ji Ubangiji, ‘wannan fāda ta zama kufai.’ ”
6 Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza,“Kyanta kamar Gileyad take a gareni,Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon.Duk da haka zan maishe ta hamada,Birnin da ba kowa ciki.
7 Zan shirya waɗanda za su hallakata.Kowannensu da makamansa,Za su sassare zaɓaɓɓun itatuwanal'ul ɗinta, a jefa su a wuta.