21 Ubangiji ya yi muku magana alokacin wadatarku.Amma kun ce, “Ba za mu kasakunne ba!”Wannan shi ne halinku tun kunasamari,Don ba ku yi biyayya da muryaUbangiji ba.
22 Iska za ta kwashe shugabanninku,Za a kai ƙaunatattunku cikinbauta,Sa'an nan za ku sha kunya ku ruɗe,Saboda dukan muguntarku.
23 Ya ku mazaunan Lebanon,Waɗanda suke zaune cikin itatuwanal'ul,Irin nishin da za ku yi sa'ad da azabata same ku,Azaba ce irin ta mace mainaƙuda!
24 “Ni Ubangiji na rantse da raina, ko da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, zoben hatimi ne a yatsan hannun damana, duk da haka zan kwaɓe shi,
25 in bashe shi a hannun waɗanda suke neman ransa, da a hannun wanda yake jin tsoronsa, wato Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da Kaldiyawa.
26 Zan jefar da shi da uwarsa a wata ƙasa inda ba a haife shi ba, a can zai mutu.
27 Amma ƙasan nan da suke marmarin komowa cikinta, ba za su koma cikinta ba.”