2 Haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya faɗa a kan makiyayan jama'arsa. “Kun warwatsar da garkena kun kore su, ba ku lura da su ba. Ni ma haka zan yi da ku saboda muguntarku, ni Ubangiji na faɗa.
3 Sa'an nan zan tattaro sauran garkena daga wuraren da aka warwatsa su, zan komo da su cikin garkensu, zan sa su hayayyafa su riɓaɓɓanya.
4 Zan sa makiyayan da za su lura da su. Ba kuwa za su ƙara jin tsoro, ko razana ba, ba kuma wanda zai ɓace, ni Ubangiji na faɗa.
5 “Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanakisuna zuwa,Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalcidaga zuriyar DawudaWanda zai ci sarauta.Zai yi sarauta da hikima,Zai aikata abin da yake daidai aƙasar.
6 A zamaninsa za a ceci Yahuza,Isra'ila kuwa za ta zauna lafiya.Sunan da za a kira shi da shi kenan,‘Ubangiji Adalcinmu.’
7 “Saboda haka, ga shi, kwanaki suna zuwa, ni Ubangiji na faɗa, sa'ad da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin ƙasar Masar ba,’
8 amma za su ce, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da zuriyar Isra'ila daga ƙasar arewa, daga kuma dukan ƙasashen da ya warwatsa su!’ Sa'an nan za su zauna a ƙasarsu ta kansu.”