11 Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al'ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba'in.
12 Sa'an nan bayan cikar shekara saba'in ɗin, zan hukunta Sarkin Babila da ƙasarsa, wato ƙasar Kaldiyawa. Zan maishe ta kango har abada, saboda zunubinsa.
13 Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abin da na faɗa gāba da ita. Dukan abin da aka rubuta a wannan littafi, wato dukan abin da Irmiya ya yi annabcinsa gāba da dukan al'umman nan.
14 Al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.’ ”
15 Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce mini, “Ka karɓi ƙoƙon ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al'umman da na aike ka gare su, su sha.
16 Za su sha, su yi tangaɗi su yi hauka saboda takobin da zan aiko a cikinsu.”
17 Sai na karɓi ƙoƙon daga wurin Ubangiji, na sa dukan al'umman da Ubangiji ya aike ni gare su, su sha daga cikinsa.