6 Kada ku bi gumaka, ku bauta musu, ku yi musu sujada, ko ku tsokane ni da ayyukan hannuwanku, sa'an nan ba zan hore ku ba.’
7 Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.
8 “Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Tun da yake kun ƙi yin biyayya da maganata,
9 zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.
10 Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu.
11 Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al'ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba'in.
12 Sa'an nan bayan cikar shekara saba'in ɗin, zan hukunta Sarkin Babila da ƙasarsa, wato ƙasar Kaldiyawa. Zan maishe ta kango har abada, saboda zunubinsa.