1 Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila. (
2 Ya rubuta wannan bayan tashin sarki Yekoniya, da uwa tasa, da bābāni, da sarakunan Yahuza, da na Urushalima, da gwanayen aikin hannu, da maƙera daga Urushalima.)
3 Ya aika da wasiƙar ta hannun Elasa ɗan Shafan, da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Zadakiya Sarkin Yahuza ya aika zuwa Babila, wurin Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Ga abin da wasiƙar ta ce.
4 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce wa dukan waɗanda aka kai bauta, wato waɗanda ya aika da su bauta daga Urushalima zuwa Babila.
5 ‘Ku gina gidaje, ku zauna a ciki, ku dasa gonaki, ku ci amfaninsu.
6 Ku auri mata, ku haifi 'ya'ya mata da maza. Ku auro wa 'ya'yanku mata, ku aurar da 'ya'yanku mata, domin su haifi 'ya'ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.