29 Sai Zafaniya firist, ya karanta wasiƙan nan a gaban annabi Irmiya.
30 Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya, ya ce,
31 ya aika wa dukan waɗanda suke zaman talala ya ce, “Haka Ubangiji ya ce a kan Shemaiya mutumin Nehelam, ‘Saboda Shemaiya ya yi muku annabci, alhali ni ban aike shi ba, ya sa ku dogara ga ƙarya,’
32 saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama'a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama'ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.