6 Ku auri mata, ku haifi 'ya'ya mata da maza. Ku auro wa 'ya'yanku mata, ku aurar da 'ya'yanku mata, domin su haifi 'ya'ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.
7 Amma ku nemi zaman lafiyar birni inda na sa aka kai ku zaman talala, ku yi addu'a ga Ubangiji saboda birnin, gama zaman lafiyar birnin shi ne naku zaman lafiyar.’
8 Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. ‘Kada ku yarda annabawanku da malamanku na duba waɗanda suke tare da ku su ruɗe ku, kada ku kasa kunne ga mafarkansu.
9 Gama annabcin da suke yi muku da sunana, ƙarya ne, ni ban aike su ba.’
10 “Ubangiji ya ce, ‘Sa'ad da kuka cika shekara saba'in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri.
11 Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.
12 Sa'an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu'a a wurina, zan kuwa ji ku.