11 Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba.
12 Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce,“Ki komo ya Isra'ila, marar aminci,Ni Ubangiji, na faɗa.Domin ni mai jinƙai ne,Ba zan yi fushi da ke ba.Ba zan yi fushi da ke har abada ba,Ni, Ubangiji na faɗa.
13 Ke dai ki yarda da laifinki,Da kika yi wa Ubangiji Allahnki,Kin kuma watsar da mutuncinki awurin baƙiA gindin kowane itace mai duhuwa.Kika ƙi yin biyayya da maganata,Ni, Ubangiji, na faɗa.
14 “Ku komo, ya ku mutane marasaaminci,Gama ni ne Ubangijinku.Zan ɗauki mutum guda daga kowanegari,In ɗauki mutum biyu daga kowaneiyali,Zan komo da su zuwa DutsenSihiyona.
15 Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi.
16 Sa'ad da kuka yawaita a ƙasar, mutane ba za su ƙara yin magana a kan akwatin alkawari na Ubangiji ba. Ba za su ƙara yin tunaninsa ko su tuna da shi, ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
17 In lokacin nan ya yi, za a kira Urushalima gadon sarautar Ubangiji, dukan sauran a'umma za su taru a Urushalima da sunana. Ba za su ƙara bin tattaurar zuciyarsu mai mugunta ba.