8 Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.
9 Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa.
10 Duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.”
11 Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba.
12 Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce,“Ki komo ya Isra'ila, marar aminci,Ni Ubangiji, na faɗa.Domin ni mai jinƙai ne,Ba zan yi fushi da ke ba.Ba zan yi fushi da ke har abada ba,Ni, Ubangiji na faɗa.
13 Ke dai ki yarda da laifinki,Da kika yi wa Ubangiji Allahnki,Kin kuma watsar da mutuncinki awurin baƙiA gindin kowane itace mai duhuwa.Kika ƙi yin biyayya da maganata,Ni, Ubangiji, na faɗa.
14 “Ku komo, ya ku mutane marasaaminci,Gama ni ne Ubangijinku.Zan ɗauki mutum guda daga kowanegari,In ɗauki mutum biyu daga kowaneiyali,Zan komo da su zuwa DutsenSihiyona.