11 Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu.Ya fanshe shi daga hannuwanwaɗanda suka fi ƙarfinsa.
12 Za su zo su raira waƙa da ƙarfi,A bisa ƙwanƙolin Sihiyona,Za su yi annuri saboda alherinUbangiji,Saboda hatsi, da ruwan inabi, damai,Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu.Rayuwarsu za ta zama kamarlambu,Ba za su ƙara yin yaushi ba.
13 Sa'an nan 'yan mata za su yi rawada farin ciki,Samari da tsofaffi za su yi murna.Zan mai da makokinsu ya zamamurna,Zan ta'azantar da su, in ba su farinciki maimakon baƙin ciki.
14 Zan yi wa ran firistoci biki dawadata,Jama'ata za su ƙoshi da alherina,Ni Ubangiji na faɗa.”
15 Ga abin da Ubangiji ya ce,“An ji murya daga Rama,Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi,Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta,ba su.
16 Ki yi shiru, ki daina kuka,Ki shafe hawaye daga idanunki.Za a sāka miki wahalarki,Za su komo daga ƙasar abokin gāba,Ni Ubangiji na faɗa.
17 Akwai sa zuciya dominki a nangaba,Ni Ubangiji na faɗa.'Ya'yanki za su komo ƙasarsu.