14 Zan yi wa ran firistoci biki dawadata,Jama'ata za su ƙoshi da alherina,Ni Ubangiji na faɗa.”
15 Ga abin da Ubangiji ya ce,“An ji murya daga Rama,Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi,Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta,ba su.
16 Ki yi shiru, ki daina kuka,Ki shafe hawaye daga idanunki.Za a sāka miki wahalarki,Za su komo daga ƙasar abokin gāba,Ni Ubangiji na faɗa.
17 Akwai sa zuciya dominki a nangaba,Ni Ubangiji na faɗa.'Ya'yanki za su komo ƙasarsu.
18 “Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yanacewa,‘Ka hore ni, na kuwa horu,Kamar ɗan maraƙin da ba shi dahoro,Ka komo da ni don in zama kamaryadda nake a dā,Gama kai ne Ubangiji Allahna.
19 Gama na tuba saboda na rabu dakai,Bayan da aka ganar da ni, sai nasunkuyar da kai,Kunya ta kama ni, na gigice,Domin ina ɗauke da wulakancinƙuruciyata.’
20 Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccenɗana ba ne?Ashe, shi ba ɗan gaban goshina bane?A duk lokacin da na ambace shi akan muguntarsaNakan tuna da shi da ƙauna.Saboda na ƙwallafa zuciyata akansa,Hakika zan yi masa jinƙai, niUbangiji na faɗa.”