37 Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya.
38 Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu.
39 Zan ba su zuciya ɗaya, da tafarki ɗaya domin su yi tsorona har abada, domin amfanin kansu da na 'ya'yansu a bayansu.
40 Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.
41 Zan ji daɗin yi musu alheri. Zan dasa su a wannan ƙasa da aminci da zuciya ɗaya.”
42 Gama haka Ubangiji ya faɗa, “Daidai kamar yadda na kawo wannan babbar masifa a kan jama'an nan, haka kuma zan kawo musu dukan waɗannan alherai da na alkawarta musu.
43 Za a sayi gonaki a wannan ƙasa wadda kake cewa ta zama kufai, ba mutum, ba dabba a ciki, wadda aka ba da ita ga Kaldiyawa.