6 Irmiya ya ce, “Ubangiji ya yi magana da ni, cewa
7 ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ”
8 Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa'an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce.
9 Sai na sayi gonar a Anatot daga hannun Hanamel ɗan kawuna, na biya shi shekel goma sha bakwai na azurfa.
10 Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma'auni.
11 Na ɗauki takardun ciniki waɗanda aka rubuta sharuɗan a ciki da wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba,
12 na ba Baruk, ɗan Neriya, ɗan Ma'aseya, a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da gaban shaidun da suka sa hannun a takardar shaidar sayen, da gaban dukan Yahudawa waɗanda suke zaune a gidan waƙafi.