1 Ubangiji ya sāke yin magana da Irmiya sa'ad da yake a kulle a gidan waƙafi.
2 Ubangiji wanda ya halitta duniya, ya siffata ta, ya kafa ta, sunansa Ubangiji, ya ce,
3 “Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”
4 Gama haka Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, a kan gidajen da suke a wannan birni, da gidajen sarakunan Yahuza, waɗanda aka rurrushe domin a yi wa garukan jigo saboda mahaurai da suka kewaye birni, da kuma saboda yaƙi.
5 “Sa'ad da ake zuwa yaƙi da Kaldiyawa gidaje za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata, gama na ɓoye wa wannan birni zatina saboda dukan muguntarsu.