1 A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya yake mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya,
2 “Ka tafi gidan Rekabawa, ka yi magana da su, ka kawo su a Haikalin Ubangiji, cikin ɗayan ɗakunan, sa'an nan ka ba su ruwan inabi su sha.”
3 Sai na ɗauki Yazaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da 'yan'uwansa, da dukan 'ya'yansa maza da dukan iyalin gidan Rekabawa.
4 Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin 'ya'yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma'aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa.
5 Sa'an nan na sa tuluna cike da ruwan inabi, da ƙoƙuna a gaban Rekabawa, sai na ce musu, “Ku sha ruwan inabi!”