15 Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.
16 'Ya'yan Yonadab ɗan Rekab sun kiyaye umarnin da kakansu ya yi musu. Amma jama'an nan ba su yi mini biyayya ba.
17 Domin haka, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce zan kawo wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima masifar da na ce zan kawo musu, domin na yi musu magana, ba su ji ba, na kira su, ba su amsa ba.”
18 Sai Irmiya ya ce wa Rekabawa, “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Tun da yake kun kiyaye dukan abin da Yonadab kakanku ya umarce ku,
19 saboda haka Yonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa magaji wanda zai tsaya a gabana ba.’ ”