15 Irmiya kuwa ya ce wa Zadakiya, “Idan na faɗa maka gaskiya za ka kashe ni, idan kuma na ba ka shawara, ba za ka karɓi shawarata ba.”
16 Sarki Zadakiya ya rantse wa Irmiya a ɓoye, ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda yake ba mu rai, ba zan kashe ka ko in bashe ka a hannun waɗannan mutane da suke neman ranka ba.”
17 Irmiya ya ce wa Zadakiya, “Haka Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, idan ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila, za ka tsira, ba kuwa za a ƙone birnin da wuta ba, kai da gidanka za ku tsira.
18 Amma idan ba ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila ba, to, za a ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa, za su ƙone shi da wuta. Kai kuma ba za ka tsira daga hannunsu ba.”
19 Sarki Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawa waɗanda suka gudu zuwa wurin Kaldiyawa. Kila a bashe ni a hannunsu, su ci mutuncina.”
20 Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.
21 Amma idan ka ƙi miƙa wuya, to, ga abin da Ubangiji ya nuna mini a wahayi.