1 Shugabannin sojoji, da Yohenan ɗan Kareya, da Yazaniya ɗan Hoshaiya, da jama'a duka, daga ƙarami zuwa babba, suka zo,
2 suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka.
3 Ka yi mana addu'a domin Ubangiji Allahnka ya nuna mana hanyar da za mu bi, da kuma abin da za mu yi.”
4 Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu'a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”
5 Sa'an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji mai gaskiya, mai aminci ya zama shaida a tsakaninmu, idan ba mu yi duk yadda Ubangiji Allahnka ya aiko ka gare mu ba.