10 ‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku.
11 Kada ku ji tsoron Sarkin Babila, shi wanda kuke jin tsoronsa. Kada ku ji tsoronsa,’ in ji Ubangiji, ‘gama ina tare da ku, zan cece ku, in kuɓutar da ku daga hannunsa.
12 Zan yi muku jinƙai in sa sarkin ya ji ƙanku, ya bar ku ku zauna a ƙasarku.’
13 “Amma idan kuka ce ba za ku zauna a wannan ƙasa ba, kuka ƙi yin biyayya da muryar Ubangiji Allahnku,
14 kuna cewa, ‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.’
15 To, sai ku ji maganar Ubangiji, ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Idan zuwa Masar kuka sa gaba don ku tafi ku zauna a can,
16 to, takobin nan da kuke jin tsoro, zai ci muku can a ƙasar Masar, yunwan nan kuma da kuke jin tsoro za ta bi ku zuwa Masar ta tsananta muku, a can za ku mutu.