3 Amma Baruk ɗan Neriya shi ne ya sa ka faɗi wannan magana gāba da mu, don ka bashe mu a hannun Kaldiyawa domin su kashe mu, ko kuwa su kai mu bauta a Babila.”
4 Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji, da dukan jama'a, ba su yi biyayya da umarnin Ubangiji, su zauna a ƙasar Yahuza ba.
5 Amma Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe sauran mutanen Yahuza duka waɗanda suka komo suka zauna a ƙasar Yahuza, daga wurin al'ummai, inda aka kora su,
6 mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya.
7 Suka zo ƙasar Masar, gama ba su yi biyayya da muryar Ubangiji ba. Suka sauka a Tafanes.
8 Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya a Tafanes ya ce,
9 “Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir'auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza,