5 Amma Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe sauran mutanen Yahuza duka waɗanda suka komo suka zauna a ƙasar Yahuza, daga wurin al'ummai, inda aka kora su,
6 mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya.
7 Suka zo ƙasar Masar, gama ba su yi biyayya da muryar Ubangiji ba. Suka sauka a Tafanes.
8 Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya a Tafanes ya ce,
9 “Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir'auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza,
10 ka kuma ce musu, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin.
11 Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi.