14 Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”
15 Sai dukan mazan da suka sani matansu sun miƙa wa gumaka hadayu, da dukan matan da suke tsaye a wurin, da dukan Yahudawan da suke zaune a Fatros, babban taron jama'a, suka ce wa Irmiya,
16 “Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba!
17 Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.
18 Amma tun da muka daina miƙa wa sarauniyar sama hadayu, da hadayu na sha, ba mu da kome, sai dai takobi da yunwa suke kashe mu.”
19 Mata kuma suka ce, “Sa'ad da muka toya waina ga siffar sarauniyar sama, muka miƙa mata hadayu, da hadayu na sha, ai, mazanmu sun goyi bayan abin da muka yi.”
20 Sa'an nan Irmiya ya ce wa dukan mutane, mata da maza, waɗanda suka ba shi irin amsan nan, ya ce,