1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma.
2 Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.
3 Masarawa suka yi ihu, suka ce,“Ku shirya kutufani da garkuwa,Ku matso zuwa wurin yaƙi!
4 Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, kuhau!Ku tsaya a wurarenku da kwalkwalia ka!Ku wasa māsunku!Ku sa kayan yaƙi!”
5 Ubangiji ya yi tambaya ya ce,“Me nake gani?Sun tsorata, suna ja da baya,An ci sojojinsu, suna gudu,Ba su waiwayen baya, akwai tsoro akowane sashi.”
6 Masu saurin gudu ba za su tsere ba,Haka nan kuma jarumi,A arewa a gefen Kogin Yufiretis,Sun yi tuntuɓe, sun fādi.