15 Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi,Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba?Domin Ubangiji ya tunkuɗe shiƙasa!
16 Sun yi ta fāɗuwa,Suna faɗuwa a kan juna,Sai suka ce, ‘Mu tashi mu komawurin mutanenmu,Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gududaga takobin azzalumi!’
17 “Ku ba Fir'auna Sarkin Masarsabon suna,‘Mai yawan surutu, wanda bai rifcizarafi ba!’
18 Ni wanda sunana Ubangiji MaiRunduna Sarki ne,Na rantse da raina, wani zai ɓullo,Kamar Tabor a cikin tsaunuka,Ko kuwa kamar Karmel a bakinteku.
19 Ya ku mazaunan Masar,Ku shirya kayanku don zuwa bauta,Gama Memfis za ta lalace, ta zamakufai,Ba mai zama a ciki.
20 “Masar kyakkyawar karsana ce,Amma bobuwa daga arewa ta aukarmata!
21 Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙane, masu yawan kitse,Sun ba da baya, sun gudu, ba sutsaya ba,Domin ranar masifarsu ta zo,Lokacin halakarsu ya yi.