15 Mai hallaka Mowab da garuruwantaya taho,Zaɓaɓɓun majiya ƙarfinta sungangara mayanka,Ni sarki, mai suna Ubangiji MaiRunduna, na faɗa.
16 Masifar Mowab ta kusato,Halakarta kuma tana gaggabtowa.
17 “Ku yi makoki dominta, ku da kukekewaye da ita,Dukanku da kuka san sunanta, kuce,‘Ƙaƙa sandan sarauta mai ikoDa sanda mai daraja ya karye?’
18 Ku da kuke zaune a Dibon,Ku sauka daga wurin zamanku maidaraja,Ku zauna a busasshiyar ƙasa,Gama mai hallaka Mowab ya zo yayi gab da ku.Ya riga ya rushe kagararku.
19 Ku mazaunan Arower,Ku tsaya a kan hanya, ku jira,Ku tambayi wanda yake guduDa wanda yake tserewa,Abin da ya faru.
20 An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.
21 “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,