18 Ku da kuke zaune a Dibon,Ku sauka daga wurin zamanku maidaraja,Ku zauna a busasshiyar ƙasa,Gama mai hallaka Mowab ya zo yayi gab da ku.Ya riga ya rushe kagararku.
19 Ku mazaunan Arower,Ku tsaya a kan hanya, ku jira,Ku tambayi wanda yake guduDa wanda yake tserewa,Abin da ya faru.
20 An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.
21 “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,
22 da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,
23 da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,
24 da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.