39 An farfashe Mowab, ta yi kuka, ta kunyata! Ta zama abin dariya da abin tsoro ga waɗanda suke kewaye da ita.
40 “Ni Ubangiji na ce,Wani zai yi firiya da sauri kamargaggafa,Zai shimfiɗa fikafikansa a kanMowab.
41 Za a ci garuruwa da kagarai dayaƙi,A wannan rana zukatan sojojinMowabZa su zama kamar zuciyar macen datake naƙuda.
42 Za a hallaka Mowab daga zamanal'umma,Domin ta tayar wa Ubangiji.
43 Tsoro, da rami, da tarko sunajiranku,Ya mazaunan Mowab,Ni Ubangiji na faɗa.
44 Wanda ya guje wa tsoro,Zai fāɗa a rami,Wanda kuma ya fito daga cikinrami,Tarko zai kama shi.Gama na sa wa Mowab lokacin dazan hukunta ta,Ni Ubangiji na faɗa.
45 “A ƙarƙashin inuwar Heshbon 'yangudun hijira suna tsaye ba ƙarfi.Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon,Harshen wuta kuma ya fito dagaSihon,Ta ƙone goshin Mowab daƙoƙwan kai na 'yan tayarwa.