23 Amma mutanen nan suna da taurinzuciya, masu halin tayarwa ne,Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.
24 A zuciya ba su cewa,‘Bari mu ji tsoron UbangijiAllahnmuWanda yake ba mu ruwan sama akan kari,Na kaka da na bazara,Wanda yake ba mu lokacin girbi.’
25 Laifofinku sun raba ku da waɗannanabubuwa.Zunubanku kuma sun hana kusamun alheri.
26 “Gama an sami mugaye, a cikinjama'ata,Suna kwanto kamar masu kafaashibta.Sun ɗana tarko su kama mutane.
27 Kamar kwando cike da tsuntsaye,Haka nan gidajensu suke cike da cinamana,Don haka suka zama manya, sukasami dukiya.
28 Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul,Ba su da haram a kan aikatamugunta,Ba su yi wa marayu shari'ar adalci,don kada su taimake su.A wajen shari'a ba su bin hakkinmatalauta.
29 “Ba zan hukunta su sabodawaɗannan abubuwa ba?Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kanal'umma irin wannan ba?