10 Za a washe Kaldiyawa,Waɗanda suka washe su kuwa za suƙoshi,Ni Ubangiji na faɗa.
11 “Saboda kuna murna, kuna farinciki,Ku da kuka washe gādona,Saboda kuma kuna tsalle kamarkarsana a cikin ciyawa,Kuna haniniya kamar ingarmu,
12 Domin haka za a kunyatar da Babilasosai, inda kuka fito.Za ta zama ta baya duka a cikinsauran al'umma,Za ta zama hamada, busasshiyarƙasa.
13 Saboda fushin Ubangiji, ba wandazai zauna a cikinta,Za ta zama kufai,Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zaiji tsoro,Zai kuma yi tsaki sabodalalacewarta.
14 “Dukanku 'yan baka, ku ja dāga, kukewaye Babila,Ku harbe ta, kada ku rage kibanku,Gama ta yi wa Ubangiji zunubi.
15 Ku kewaye ta da kuwwar yaƙi!Ta ba da gari,Ginshiƙanta sun fāɗi.An rushe garunta,Gama wannan sakayya ce taUbangiji.Ku sāka mata, ku yi mata kamaryadda ta yi.
16 Ku datse wa Babila mai shuka,Da mai yanka da lauje a lokacingirbi.Saboda takobin azzalumi,Kowa zai koma wurin mutanensa,Kowa kuma zai gudu zuwaƙasarsa.”