57 “Zan sa mahukuntanta, da masuhikimarta,Da masu mulkinta, dashugabanninta,Da sojojinta su sha su yi maye.Za su dinga yin barcin da ba za sufarka ba,”In ji Sarkin, mai suna Ubangiji MaiRunduna.
58 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce,Za a baje garun nan na Babila maifāɗiZa a kuma ƙone dogayenƙyamarenta da wuta.Mutane sun wahalar da kansu abanza.Sauran al'umma sun yi wahala kawaidomin wutar lalata.”
59 Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma'aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi.
60 Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila.
61 Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan.
62 Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’
63 Sa'ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa'an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis.