25 Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai 'yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su.
26 Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babila a Ribla,
27 Sarkin Babila kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat.Haka aka tafi da mutanen Yahuza bautar talala.
28 Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa dubu uku da ashirin da uku (3,023).
29 A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima ɗari takwas da talatin da biyu.
30 A shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa kuma, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa ɗari bakwai da arba'in da biyar. Jimillarsu duka kuwa dubu huɗu da ɗari shida ne (4.600).
31 A shekarar da Ewil-merodak ya zama Sarkin Babila, sai ya nuna wa Yekoniya Sarkin Yahuza alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yekoniya bauta.