7 Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa'ad da Kaldiyawan take kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.
8 Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki Zadakiya, suka ci masa a filayen Yariko. Dukan sojoji suka yashe shi.
9 Da aka kama Zadakiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babila ya yanke masa shari'a.
10 Ya kuwa kashe 'ya'yan Zadakiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuza a Ribla.
11 Sa'an nan ya ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babila inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.
12 A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.
13 Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.