5 “ ‘Idan dai kun gyara hanyoyinku, da ayyukanku bisa kan gaskiya, idan da gaskiya kuke aikata adalci ga junanku,
6 idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka,
7 sa'an nan zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasa wadda tuni na ba kakanninku har abada.
8 “ ‘Ga shi, kun amince da maganganu na ruɗami, marasa amfani.
9 Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba'al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba?
10 Sa'an nan za ku zo ku tsaya a gabana a wannan Haikali, wanda ake kira da sunana, ku ce, “An cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan banƙyama?
11 Wannan Haikali wanda ake kira da sunana ya zama kogon mafasa a idanunku. Ga shi, ni da kaina na gani.’ ” in ji Ubangiji.