7 sa'an nan zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasa wadda tuni na ba kakanninku har abada.
8 “ ‘Ga shi, kun amince da maganganu na ruɗami, marasa amfani.
9 Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba'al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba?
10 Sa'an nan za ku zo ku tsaya a gabana a wannan Haikali, wanda ake kira da sunana, ku ce, “An cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan banƙyama?
11 Wannan Haikali wanda ake kira da sunana ya zama kogon mafasa a idanunku. Ga shi, ni da kaina na gani.’ ” in ji Ubangiji.
12 “ ‘Ku tafi Shilo wurin da na fara zaunar da sunana, ku ga abin da na yi mata saboda muguntar mutanena Isra'ila.
13 Yanzu kuwa saboda kun aikata waɗannan al'amura, sa'ad da na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne ba, sa'ad da na kira ku, ba ku amsa ba,