1 Wannan shi ne saƙo a kan Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa daga wurin Allah.
2 A kan tudun da yake faƙo ka kafa tutar yaƙi, ka ta da murya ka ba mayaƙa umarni, ka ɗaga hannu, ka ba su alamar kama yaƙi a ƙofofin birni mai alfarma.
3 Ubangiji ya kira mayaƙansa masu jin kansu, masu ƙarfin zuciya, domin su yi jahadi, su hukunta wa waɗanda suke fushi da su.
4 Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama'a. Amon al'ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi.
5 Suna zuwa daga manisantan ƙasashe, daga kan iyakokin duniya. Ubangiji yana zuwa da fushinsa, ya lalatar da dukan ƙasar.
6 Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka.